<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><title>Maƃulƃula Na Ruwan Rai, Kishi Zai Kashe Ni LW52</title>
<lyrics>[V1]
 1) Maƃulƃula na ruwan rai, Kishi zai kashe ni,
 Zubo da ruwan daɗinka domin ka rayad da ni.

[V2]
 2) Raina ya zama busasshe, ƙarfi ya gaza ma,
 Ka shayad da ni da ruwanka, ya Allah, Ubana.

[V3]
 3) Maƃulƃula na Allahna, daga kursiyi ka zo,
 Ka ƃullo cikin zuciyata, in ka yarda yanzu.

[V4]
 4) Kai ne mai ikon warkarwa, kai ne mai ba da rai,
 Salama da alherinka su na ke so ƙwarai.

[V5]
 5) Ka ba ni irin ruwan nan wanda zai ƃulƃula
 A cikin zuciyata sosai, rai na har abada.</lyrics>
<hymn_number>52</hymn_number>
</song>